2016-08-26

 Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta karabi bakuncin ‘yan jaridu a ranara Alhamis 25 ga watan Agusta a inda ta kewaya da su inda ta ke tsare wadanda suka fada kwamarta, ga kuma hotunan wasu daga cikin wuraren kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na yanar gizo



Shalkwatar hukumar a Abuja

Shugaban Hukuymar EFCC ne Ibrahim Magu ne ya kewaya da ‘yan jaridu inda hukumar ke ajiye wadanda ta ke tsare da su a shalkwatarta da ke Abuja.



wasu daga cikin inda ake tsare mutane a hukumar

KU KARANTA: EFCC ta soma binciken Jonah Jang na Plateau



KU KARANTA: Nenadi ta sake shiga hannun EFCC a Gombe

Shugaban hukumar na kewayawa da ‘yan jaridu a yayin ziyarar

Shugaban ya nunawa ‘yan jarida wasu manya-manya wurin tsare mutane a karkashin ginin hukumar mai hawa hudu da da aka yiwa lakabi da Idiagbon House a unguwar Wuse II a Abuja.

An kuma nunawa ‘yan jaridun inda ake tuhumar wadanda ake tsare da su, da dakin shan maganin wadanda aka tsare na bayar da taimakon farko ga wadanda suka kamu da rashin lafiya.

Hukumar ta EFCC na da izinin kamawa tare da tsare duk wanda ta ke zargi da laifin yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, har sai ta gudanar da bincike ta kuma gurfanar a shi a gaban kotu, cikin wadanda hukumar ta tsare a ‘yan kwanakin nan, sun hada da manyan ‘yan siyasa ciki har da  wasu tsaffin ministoci a gwamnatin da ta wuce.

The post Dakunan manyan bakin EFCC a Abuja (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Show more